Bayan barkewar cutar kwalara a jihar Maradi sai gashi ta kuma bulla a gundumar Konni dake cikin jihar Touha a jamhuriyar Niger.
Kawo yanzu mutane 27 ne suka kamu yayinda uku suka rigamu gidan gaskiya. Malam Hassan Haruna mai kula da sha'anin sadarwa a babban asibitin Konni shi ya sanar da hakan. Ya ce "gundumar Konni mun shiga cikin annoba na cutar kwalara". Ya ci gaba cewa wuraren da suka aika a yi masu bincike a yankin an samu kawayar kwalara a biyar lamarin da ya ce ko daya ne aka samu an shiga cikin annoba.
Kwalarar ta fi kamari a garin Konni da Dosa. Malam Hassan ya tabbatar da mutuwar mutane uku amma sauran an sallamesu baicin wasu uku da suka rike ana ci gaba da yi masu magani.
Yanzu dai malaman asibiti na ci gaba da yin kira tare da gargadin jama'a, musamman mazauna cikin birnin Konni, da su dauki matakan rigakafi game da cutar. Kazalika Malam Hassan Haruna ya kira masu hannu da shuni da su taimakawa mara sa karfi saboda wai yaki da cutar ba na asibiti kawai ba ne. Yaki ne na kowa da kowa, inji Malam Hassan.
A saurari karin bayani a rahoton Haruna Mamman Bako.
Facebook Forum