Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Bude Makarantu Ga Dalibai a Najeriya Domin Yin Jarrabawar WAEC


Yadda ake auna zafin jikin wasu dalibai a Afirka ta Kudu
Yadda ake auna zafin jikin wasu dalibai a Afirka ta Kudu

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za a bude makarantu a ranar 4 ga watan Augusta ga daliban da ke ajin karshe a makarantun Sakandare domin rubuta jarrabawar WAEC.

Gwamnatin ta bayyana matakin ne a cikin watan sanarwar da ma'aikatar ilimi ta fitar a yau Litinin wacce ke dauke da sa hannun daraktan yada labarai na Ma'aikatar, Ben Bem Goong.

Wannan matakin ya biyo bayan shafe sa'o'i ana tattaunawa a yau tsakanin ma'aikatar ta ilimi da kwamishinonin ilimi da kuma masu ruwa da tsaki a harkokin ilimi a kasar.

Sanarwar ta bayyana yadda aka umarci 'yan ajin karshe da su koma makaranta da an kammala bikin sallah mai zuwa domin shirin yin jarrabawar wacce za a fara a ranar 17 ga watan Augusta.

A tattaunawar tasu, an Kuma bayyana cewa makarantu za su bukaci taimako daga gwamnatin tarayya wajen iya budewa cikin gaggawa.

Makarantu a kasar daga matakin farko zuwa karshe sun shafe watanni a garkame saboda kokarin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

A cikin makonnin da suka gabata gwamnatin ta bayyana cewa ba za a gudanar da jarrabawar WAEC ba saboda cutar, amma yanzu gwamnatin ta sauya matsayarta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG