Firai Ministan kasar China, Li Leqiang ya kai ziyara birinin Wuhan a yau Litinin, domin haduwa da jami’an lafiya da kuma duba matakan da aka dauka game da barkewar cutar ta Corona virus da ta kashe mutune 81.
Wuhan, shi ne birnin da cutar ta barke, kuma an gindayawa mutanen birnin da wasu sauran garuruwa tsauraran matakan zirga zirga yayin da gwamnati ke kokarin dakile yaduwar cutar.
Jami’ai sun dauki karin wasu matakai a jiya Lahadi, da suka hada da kara hutun sabuwar shekara da kwanaki 3 don su rage cudanyar mutane da yawa.
Li Bin, wanda shi ne kwamishinan lafiya a China, ya ce, "Wannan cuta sabuwa ce a gare mu, ba mu da cikakken bayani game da ita kuma har yanzu ba mu samu kwararan bayanai game da ita ba."
Sabbin alkaluman da jami’an hukumomin kiwon lafiya na China suka tattara sun hada har da sama da mutune 2,700 da suka kamu da cutar.
Facebook Forum