Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19 Ta Cimma Wani Zango Na Tarihi


Wata ma'aikaciyar jinya a Amurka
Wata ma'aikaciyar jinya a Amurka

Annobar coronavirus ta cimma wani zango na tarihi, ta yadda wandanda aka tabbatar sun kamu da cutar a duk duniya su ka kai miliyan 12, bisa ga alkaluman jami’ar Johns Hopkins dake bin diddigi game da cutar ta yanar gizo.

Amurka ce take kan gaba a duniya da yawan wadandan aka tabbatar sun kamu da COVID-19 mutum miliyan uku da dubu hamsin da hudu da dari shida da casa’in da biyar; wato kashi uku cikin dari na yawan wadanda su ka kamu da cutar a fadin duniya, wanda ya hada da sabbin kamuwa sama da dubu sittin a jiya Laraba, wanda shi ne adadi mafi yawa na masu kamuwa da cutar a wuni guda tun somawar annobar.

Akalla jihohi biyar da suka hada da Carlifornia, Texas, Tennessee, West Virginia da Utah sun bayyana sabbin alkaluman masu kamuwar cutar jiya Laraba, yayin da wasu jihohin da dama suka bayyana adadin sabbin masu kamuwa da cutar mai yawa cikin kwanaki 7. Jami’an lafiya a Arizona, California, Florida da Texas sun yi gargadi cewa, sashin gobe da nisa a asibitoci a fadin jihohin sun cika ko kuma sun kusan cika.

Wani wanda ke dauke da cutar Coronavirus a kasar Indiya
Wani wanda ke dauke da cutar Coronavirus a kasar Indiya

A wani bangaren kuma, mazauna birnin Australiya na biyu a girma wato Melbourne, sun shiga kullen mako shida da ya fara tun tsakar daren jiya Laraba, a dalilin hauhawar sabbin kamuwa da cutar COCID-19. An baiwa da mazauna birnin umarnin zama a gida in banda masu zuwa makaranta, aiki, asibiti ko kuma masu zuwa cefanen kayan abinci.

Tuni jami’ai suka kafa dokar zama a gida a unguwanni a kalla 30, kana, a sanya takunkumin kulle a wasu gidajen haya 9, inda mutane sama da dubu 3 ke zaune inda aka gano mutum 23 dauke da cutar COVID-19 tsaknin gidaje 12.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG