Kamfanin Walt Disney zai sake bude shahararren filin shakatawar yara na Disneyland Paris a ranar 15 ga watan Yuli.
Kwanaki kadan kenan bayan ranar da ya bayyana cewa zai bude filayensa a Amurka.
Shugabar kamfanin Natacha Rafalski ta ce "za mu bude filayen Disneyland Park da Walt Disney Studios Park da Disney's Newport Bay Club da kuma Disney Village."
Dama dai kamfanin ya rufe filayensa tun a watan Janairun shekarar 2020 yayin da cutar Coronavirus ta fara mamaye duniya, lamarin da ya janyo aka kakkaba dokokin takaita zirga-zirga a yawancin wurare.
A cikin watan da ya gabata ma, Disney ya ce zai bude filayensa a Amurka, ciki harda filinsa mafi girma a duk fadin duniya na Walt Disney World da ke jihar Florida.
Bude wadannan filayen lafiya zai zamo wa Disney da ma Duniya gabadaya babban nasara yayin da gwamnatoci da kamfanoni ke kokarin ganin yadda zasu bude wurare duk da cewar har yanzu Coronavirus na ci gaba da zama barazana.
Facebook Forum