Indiya, Faransa da Najeriya na daga cikin kasashen da shugabanninsu suka tsawaita dokar hana fita da nufin dakatar da yaduwar cutar coronavirus, yayin da adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a duniya ya cike miliyan biyu.
A yayin da yawan waddanda suka kamu da cutar a Indiya suka haura 10,300, Firayim Ministan kasar Narendra Modi ya bada sanarwa a yau Talata cewa, za a tsawaita dokar hana zirga-zirga har zuwa 3 ga watan Mayu.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya gabatar da wani jawabi ta gidan talabijin a daren ranar Litinin da ta gabata, yana cewa dokar hana fita a kasar zata kai zuwa 11 ga watan Mayu, wanda a lokacin ne hukumomi zasu fara bude makarantu.
Ya kara da cewa “a ainihin kasar ta Faransa da yankunanta na ketare lamirin yayi kamari sosai ta yadda ya fi karfin gwamnati”. Don haka ya ce, wajibi ne a ci gaba da kokarin kafa dokoki ta yadda za a iya cetar rayukan jama’a.
Facebook Forum