Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Ana Ci Gaba Da Jinyar Firayim Ministan Burtaniya a Asibiti


Firayim Ministan Burtaniya Boris Johnson, wanda ya kamu da cutar coronavirus a makon da ya gabata na ci gaba da zaman jinya a asibiti, bayan da aka kwantar da shi domin karin gwaje-gwaje da samun kulawa, sakamakon zazzabi mai zafi da yake fama da shi.

Ofishin Firayim Ministan ya bayyana wannan a matsayin “matakin kariya” ya kuma ce har yanzu shi ke jagorantar harkokin gwamnatin kasar.

Burtaniya dai ta kasance daya daga cikin kasashe na baya-bayan nan da annobar ta fi kamari, inda ko a jiya Lahadi rahotanni sun bayyana cewa mutane 600 sun mutu.

Sauran sassan kasashen Turai kuwa sun fara samun ci gaba bayan makonnin da aka shiga cikin halin kaka-na-kayi, wanda hakan ya sa gwamnatoci saka dokokin hana zirga-zirga da zummar dakile yaduwar annobar.

Kasar Italiya da aka fi samun mace-mace, ta bayyana adadi mafi karanci na wadanda suka mutu, inda Spain ita kuma ta bayyana samun raguwar adadin mace-mace da kuma sabbin kamuwa da cutar.

A nan Amurka, jihohin Oregon da Washington dake arewa maso yammacin kasar sun ce zasu aika da dubban na’urorin taimakawa masu fuskantar matsalar numfashi zuwa jihar New York, jihar da aka fi tsananin bukatarsu, kasancewar ita ce ta fi shafuwa sosai da annobar a kasar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG