Kasar Bolivia da ke Amurka ta Yamma ta kara tsaurara matakin hana zirga-zirga da aka dauka domin shawo kan yaduwar cutar coronavirus.
Shugabar kasar ta rikon kwarya Jeanine Anez, ta ce dokar ta-bacin da aka sanya akan lafiyar al’umma za ta soma aiki da karfe 12 na daren Alhamis, har ya zuwa ranar 15 ga watan Afrilu.
Hakazalika, matakin ayyana dokar ta-bacin ya kara tsawaita rufe iyakokin Bolivia zuwa ranar 15 ga watan Afrilu, makwanni 2 bayan wa’adin da aka shata na farko. Anez ta ce ba wanda za’a bari ya shiga ko ya fita kasar a cikin wannan lokacin.
Shugabar ta kara da cewa, ayyana dokar ya zama wajibi saboda wasu mutane basa bin ka’idar da aka shata ta killacewa tsawon kwanaki 14, wanda hakan ka iya jefa jama'a cikin hadarin kamuwa da cutar.
Sabon tsarin ya tanadi cewa mutum daya kacal daga kowanne iyalin gida ne zai iya fita daga karfe 7 na safe zuwa 12 na rana a ranakun aiki. Kasar ta Bolivia tana da mutum 30 da aka tabbatar sun kamu da cutar ta coronavirus.
Facebook Forum