China ta dage dokar hana zirga-zirga a gundumar Hubei, inda annobar cutar coronavirus ta soma barkewa, a yayin da hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta yi gargadin cewa Amurka za ta iya zama kasa ta gaba da annobar zata yi kamari.
Ga baki daya China ta sami gagarumin ci gaba a yaki da cutar, bayan aiwatar da tsauraran matakan killace mutane a gida da kare yaduwar cutar. Jami’an lafiya na China sun ba da sanarwar sababbin kamuwa da cutar 47, dukan su suna cikin mutanen da suka dawo daga wasu kasashe.
Amurka tana samun karin yaduwar cutar cikin sauri a ‘yan makonnin nan, wanda ya bada adadin masu cutar a kasar har 55,000 da aka tabbatar ya zuwa safiyar yau Laraba, tare da mutane 700 da suka mutu.
Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a jiya Talata, cewa yana bukatar ganin al’amura sun daidaita nan da ‘yan makwanni kalilan, yayin da jami’an kiwon lafiya ke cewa yin wani abu a halin yanzu tamkar riga malam masallaci ne, to amma sun dage akan ci gaba da matakin nisanta mutane da juna, ta yadda ba za su yada cutar ba.