Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Coronavirus: Nijar Ta Garkame Kofofinta


Shugaba Issouhou Mahamadou
Shugaba Issouhou Mahamadou

Mahukunta a Jamhuriyar Nijar sun dauki wasu sabbin matakai domin hana bullar annobar coronavirus.

Matakan sun hada da dakatar da saukar jiragen sama da kuma rufe iyakokin kasa na tsawon makonni biyu.

Shugaban kasar Issouhou Mahamadou ne ya bayyana hakan yayin wani jawabin da ya gabatar a daren jiya.

A lokacin da yake gabatar da jawabin nasa ya fara ne da nuna damuwa dangane da yadda kasashen duniya suka shiga halin rudani sanadiyyar annobar Coronavirus.

Bisa dalilin hakan ne ya ga ya dace a dauki matakan riga-kafi a kasashen da har yanzu ba a samu bullar wannan cutar ba.

Shugaba Issouhou ya ce filayen jiragen saman kasa da kasa na Yamai da Zinder za su kasance a rufe har na tsawon makonni biyu daga ranar 19 ga watan Maris.

Ya Kuma kara da cewa, za a iya tsawaita wannan mataki idan bukatar hakan ta taso.

Wannan matakin dai bai shafi jiragen likitoci da na sojoji da na dakon kaya ba.

Haka su ma iyakokin kasar za su kasance rufe har na tsawon makonni biyun daga ranar 20 ga watan nan amma motocin dakon kaya za su iya shiga da hajoji a tsawon wannan lokaci.

Gwamnatin ta Nijar ta kuma yanke shawarar rufe ilahirin makarantun boko daga ranar 20 ga watan nan na Maris.

Hakan ya sa aka bukaci iyaye da su kula da ‘ya'yansu yayin da aka umurci gidajen sayar da barasa da gidajen rawa da na sinima da dukkan wuraren wasannin nishadi su rufe daga yau Laraba 18 ga watan Maris.

Shugaban ya ce daga yanzu an haramta taron mutanen da yawansu ya zarce 50.

Wannan mataki bai bar taron bukukuwan suna ba ko bikin aure da dai wasu shagulgula makamantansu.

Shugaba Issouhou ya kuma ce ana ci gaba da tattaunawa da shugabanin addinai domin duba ta inda za a bullowa wuraren gudanar da ibada.

Kawo yanzu kasar Nijar ba ta cikin kasashen da hukumar lafiya ta duniya ta bayyana a matsayin wadda aka samu bullar wannan annoba.

Amma hukumomi sun umarci kasuwanni da manyan shagunan sayar da kayan alatu da gidajen cin abinci su mutunta matakan tsaftace muhallansu.

Sa'anan an tilasta barin tazarar akalla mita daya tsakanin kowane mutum a wurare makamantan wadannan.

Saurari cikakken rahoton nan a sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG