Yawan taimakon da mutum zai samu ya danganta ne ga yawan kwayoyin da yakan ci, a fadar wannan rahoton. Sun sami karfin gwiwar fadar haka ne sakamakon binciken da suka yi a kan ma’aikatan jinya da sauran ma’aikatan lafiya wadanda aka yi da gudanar da bincike akan su har na fiye da shekaru 20.
Cutar zuciya da kansa sukan yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane milyan guda a duniya cikin kowace shekara.
Kungiyar bincike da ake kira da turanci International Tree Nut Council Nutritional Research and Educational Foundation wato, gidauniyar kasa da kasa ta bincike da ilimantarwa akan abinci da itatuwa masu kwaya, sune suka biya domin buga wannan rahoton wanda kuma mujallar magani ta New England ta buga.
Wannan binciken ya hadu da wadansu binciken da suka nuna cewa cin irin wannan abincin a kai akai zai iya kawo raguwar hadarin rashin lafiya kamarsu cutar zuciya, kansa da kuma cutar sikari irin ta kashi na 2.
Jeffrey Blumberg, wani mamba na kungiyar binciken abinci da tsufa ta USDA dake Jami’ar Tufts ta Boston yace, “a da, ana kyamar abincin dangin su gyada domin suna kunshi da mai, amma yanxu bayan shekaru ashirin an gane cewa abinci ne mai kara lafiya.”
Blumberg yace, “Kamar yadda ada aka ki jinin kofi da kwai ne dake zama matsala ga zuciya, kwayoyi dangin su gyada suna da mai, sai dai kuma suna da mai wanda yake da amfani ga jiki kwarai.”
Rahotonnin da aka yi amfani da su a cikin wannan binciken sun fito daga wani bincike da har yanzu ake kan gudanaswa wanda ya kunshi mata wajen 76,000 wadanda kuma ma’aikatan jinya ne da kuma maza wajen 42,000 wadanda ake duba su akai akai a matsayin gwajin lafiyar su. Binciken ya hada da wadansu tambayoyi inda mutanen ke bayyana irin abincin da suke ci.