Masu bincike daga Jami’ar Haifa a kasar Isra’ila sunce binciken da akayi akan dabbobi da mutane, ya nuna cewa matan da suka sha wahala tun kamin suyi ciki zasu iya samun wannan matsalar ga jariransu.
A karshen shekarar da ta wuce, kungiyar yada labaran magunguna ta bada labari akan binciken da ya nuna cewa yaran da iyayen dake cikin matsuwa sosai suka haifa, sunfi samun matsalar wannan ciwon.
Wani binciken ya nuna cewa jariran da aka haifa ga mata wadanda suka sha wahala a rayuwarsu sunfi samun karuwar wahalar rayuwa da karuwar CRF1 (wata kwayar hallita da ta shafi damuwa da matsuwa) a lokacin haihuwa.
Har yanzu, masu bincike suna nan suna ta kokarin gano dalilin da yasa matsuwar iyaye ke haifar da wannan damuwar domin taimakawa al’umma ta nan gaba.