Washington DC —
Sabon shirin ya duba korafin wasu jami’an ‘yan sanda da su ka share yawancin shekarun su su na aiki a Maiduguri jihar Borno, musamman ma lokacin da a ka samu illar ‘yan Boko Haram.
Kamar wasu takwarorin su a wasu yankuna, ‘yan sandan sun ce sun yi aiki na tsawon shekaru 35 inda su ka yi ritaya a 2018.
Sun tinknari shirin CIKI DA GASKIYA su na masu cewa kudin karin albashi da a ka yi mu sun a tsawon wata 8 sun makale kuma yanzu sun zama ‘yan fansho inda karfin su ya kare ga dawainiyar gida da yara a makaranta.
Amma, shugaban kwamitin yan sandan na Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Halliru Dauda Jika, ya sha alwashin duba batun da zarar Majalisa ta koma aiki bayan zabe:
Ayi sauraro lafiya: