Wannan mataki da kasar China ta dauka zai yi karin haraji zuwa kashi 25 cikin 100 akan kayan Amurka iri 106 da suka hada da waken soya, jiragen sama da motoci.
Ma’aikatar kasuwancin China ta ce lokacin da matakan na ta za su fara aiki ya dogara ne akan lokacin da harajin kasar Amurka kan hajjojin China suka soma aiki.
A cikin watan jiya ne, shugaban Amurka ya bayyana yadda Amurka za ta yi karin haraji na biliyan 50 ga kayan kasar China.
Sannan kuma jiya Talata sai ga shi hukumomin kasuwanci na Amurka sun saki wani jerin samfurin kayan China guda 1,300 wadanda suka hada da jiragen sama, kayan kiwon lafiya da kayayyakin watsa labarai da abin ya shafa.
Facebook Forum