Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cleveland: An Cafke Masu Zanga Zanga 71


'Yan sanda suna tisa keyar wasu masu zanga zanga a birnin Cleveland
'Yan sanda suna tisa keyar wasu masu zanga zanga a birnin Cleveland

A birnin Cleveland na Amurka, kura ta lafa bayan da zanga zanga ta barke a lokacin da wata kotu ta wanke wani dan sanda farar fata daga zargin kisan wasu babaken fata biyu da ya auku a shekarar 2012.

‘Yan sanda sun cafke mutane 71a birnin Cleveland na Amurka, a lokacin zanga zangar da ta barke bayan da wata kotu ta wanke wani dan sanda farar fata daga zargin kisan wani mutum bakar fata tare da matarsa a shekarar 2012.

A yau Lahadi kura ta lafa a birnin, bayan zanga zangar da ta barke a daren jiya Asabar.

A yinin Asabar din ne, wani alkali ya wanke Michael Brelo daga zargin, wanda ya harba harsashai goma sha biyar na karshe daga cikin 135 da ‘yan sanda suka harba akan Timothy Russel da matarsa Melissa Williams a lokacin da suke cikin motar da suke kokarin tserewa.

Sai dai alkalin ya ce babu wata hujja da ta nuna cewa harsashan Brelo ne suka kashe mutanen biyu, duk da cewa ya hau gaban motar a lokacin da yake harbin.

Sai dai duk da wannan hukunci da aka yanke a jiya, hukumomin Cleveland sun riga sun biya iyalan mamatan biyu kudin diyya na dala miliyan 1.5 na shari’ar kisan da aka yi bisa kuskure.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG