Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Mayarwa Amurka Martani Akan Karin Kudin Fito


Shugaban China Xi Jinping
Shugaban China Xi Jinping

Yaki a fannin kasuwanci tsakanin Amurka da China na kara ta'azzara saboda China ma ta mayar da martani bisa ga karin kudin fito da Amurka ta yi inda ita ma ta kara akan kayayyakin dake shigowa kasarta daga Amurka

Kafar yada labarai ta kasar China ta mayar da martani akan matakin harkokin kasuwancin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka game da Chinan ta wasu hanyoyi daban.

Sailin da kasar ta China ke tir da matakin da shugaban na Amurka ya dauka , ta yi anfani da kafar yada labaran ta domin kwantar da hankulan ‘yan kasuwanta, kana ta bayyana damuwarta akan irin yadda hakan zai yi tasiri ga tattalin arzikin ta.

A shafin bayyana ra’ayin jaridar nan da ake kira PEOPLE’S DAILY,ta bayyana cewa kara kudin fito ta hannu guda kuma a bangare guda gwamnatin ta Trump tana bukatar a sasanta, wannan tamkar bayar wa da hannun dama ne kuma a karbe da hannun hagu

Jaridar taci gaba da cewa sai dai duk a karshe kasar ta China za ta yi galaba kan wannan tsarin na munafunci da Amurka ke tsarawa. Haka kuma China ba za ta mika wuya ga wannan barazanar ba.

Yanzu haka dai kwanan nan China ta kara labta wani karin harajin da yakai kashi 25 akan kayayyakin da kudin su ya kai har dala biliyan 60 na kayayyakin Amurka. Wannan mayar da martAni ne ga shirin da gwamnatin shugaba Trump ta shirya na karin kashi 25 akan kayayyakin kasuwanci na dala biliyan dari 2 na kasar China da ake shigowa dasu Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG