A yau Litinin kasar China ta bude wani asibiti mai gadaje dubu daya, wanda aka gina cikin gaggawa domin taimakawa kokarin da hukumomin yankin ke yi, na dakile yaduwar cutar Coronavirus da ta kama sama da mutune dubu goma sha-bakwai, bayan haka ta hallaka wasu 361.
Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce, akwai fargaban mutanen da su ka kamu da cutar, za su karu yayin da ake ci gaba da karbar sakamakon gwaje-gwajen da aka gudanar a kan cutar.
Cutar ta fi kamari a kasar China, amma kuma an samu kimanin mutune 153 da suka kamu da cutar a wasu kasashe 23. A jiya Lahadi, an samu mutum na farko da ya mutu sakamakon cutar a kasar Philippines bayan China.
Hukumomin China sun yi kokarin dakile yaduwar cutar ta hanyar hana zirga-zirga a wasu yankunan kasar, tare da kara hutun sabuwar shekarar gargajiyar kasar, domin takaita alakar mutane a makarantu da kuma wuraren da taruwar jama'a.
A yau Litinin ne kuma a kasar Vietnam, aka sallami wata mata da ta kamu da cutar ta Coronavirus, ita ce ta farko da aka sallama daga asibiti.
Facebook Forum