A duk shekara a Amurka idan bikin Kirsimeti ya gabato musammam ma cikin wata Disamba, mutane na zuwa shaguna domin sayen kayayyaki harma su kanyi wannan saye saye ta kan yanzar gizo, hakan yasa ake kawo musu kayan har kofar gidajensu.
Wasu lokuta masu kawo kayan basa samun mutane a gida hakan yasa sukan ajiye sakon a kofar gidajen mutane. Irin wannan lokaci dai yayi fice domin barayi kan zagaya unguwowi suna sace duk kayan da suka gani an ajiye a kokar gida, wato idan mutum baiyi sa’a ba to tabbas ba zai taras da kaya na jiransa ba.
Dalilin hakane yasa wasu mutanen wata unguwa a jihar Utah dake Amurka, suka fara ‘dana tarko don batawa barayi rai. Suka fara ajiye kwalaye ‘dauke da kaya marasa amfani a kofar gidajensu domin su kawar da matsalar sata a unguwar.
Wani ‘dan Unguwar yace sun fara zuba tsoffin kayayyakin sawa da ma sauran tarkace cikin irin kwalayen da akan kaiwa mutane kayan da suka saya gidajensu suna ajiyewa a kofar gida. Suna kuma amfani da boyayyiyar na’urar ‘daukar hoto mai motsi, domin kama barawo cikin aiki.
Mutanen unguwar dai sunce burinsu ba na kama barayin bane domin wannan aiki jami’an tsaro ne, su dai burinsu shine su batawa barayin rai har su dai na satar kayayyakin su domin idan barawo ya saci kwali yaje yaga ya saci shara da tarkacen banza, to ba zai kara dawowa ba.
Amma jami’an ‘yan sanda sunce su basa son mutanen unguwar su shiga cikin halin hatsari, sun basu shawarar su rika amfani da na’urar ‘daukar hotan bidiyo a maimakon abinda suke yi. Sun kuma basu shawarar su rika zuwa ofisoshin masu dakon kaya domin karbar kayayyakinsu da suka saya ta yanar gizo, domin rage ire iren wannan matsalolin.