‘Yan bindiga da ba’a tantance ko su wanene ba, sun bude wuta akan wata majami’a a gabashin kasar Burkina Faso a jiya Lahadi, inda su ka kashe akalla mutane 14.
Jamai’ai sun ce an kai harin ne a garin Hatoukoura da ke kusa da iyaka da kasar Jamhuriyyar Nijar.
Sojoji na farautar ‘yan bindigar da suka arce a kan babura, bayan sun harbe masu ibadar jiya Lahadi.
Sai dai har I zuwa lokacin rubuta wannan labarin, ba wanda ya dauki alhakin kai harin, to amma ana dora alhakin harin kan masu tsattsauran ra’ayin addinin Islama.
Kiristoci da mabiya wasu addinai na zaune lami lafiya a kasar mai rinjayen Musulmai, har sai lokacin da aka kai wasu hare-hare da ake kyautata zaton mayakan jihadi suka kai, daga makwabciyar kasar Mali a bara, wadanda suka yi sanadiyyar salwantar daruruwan rayuka.
Facebook Forum