A hirar da wakiliyar sashin hausa VOA Baraka Bashir da wani kwararren likita Dr. Nasir Isma’il Jinjiri likitan kwakwalwa na asibitin koyarwa dake sokoto ya bayyana yadda ake kamuwa da cutar Spinal bifada.
Haihuwar jinjiri da wata tawaya ko wadda akafi sani da SPINAL BIFADA a turance, masana sun bayyana cewa wannan yana aukuwa ne sakamakon tabuwar wata lakka a lokacin da mace ta sami juna biyu a farkon kwanaki ashirin da biyar zuwa da takwas .
Wannan cutar dai tana sanadin haihuwar jariri da kumburi a keyar sa ko a gadon bayan sa da kuma wasu sassan jiki da kuma kwakwalwar dan tayin da ke ciki.
Masana sun bayyana cewar rashin shan wasu magunguna masu sanadarin Polic Acid da na Karin jinni da na karawa mai juna biyu kuzari da kuma kare dan tayin dake cikinta domin kariya daga cutar yana sa cutar ta kama jariri kuma tayi masa illa.
##caption: Likita na duba wata mai juna biyu. ##