Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Borno Ta Karbi Rigakafin Kwalara Daga UNICEF

Wata mai jinya rike da allurar riga-kafin Astrazeneca a Najeriya
Wata mai jinya rike da allurar riga-kafin Astrazeneca a Najeriya

Sanarwar da ofishin UNICEF na Najeriya ya fitar a jiya Alhamis tace asusun ya samar da rigakafin ne domin tabbatar da al’ummar Borno sun samu dauki cikin lokaci.

Gwamnatin jihar Borno ta karbi wasu alluran rigakafin kwalara daga asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da wasu hukumomin bada agaji domin baiwa al’ummarta kariya daga cutar.

Sanarwar da ofishin UNICEF na Najeriya ya fitar a jiya Alhamis tace asusun ya samar da rigakafin ne domin tabbatar da al’ummar Borno sun samu dauki cikin lokaci.

“Jami’in UNICEF Dr. Rownak Khan ya ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira na Gubio domin ganin halin da mata da yaran da iftila’in ambaliyar ruwa da annobar kwalara suka daidaita ke ciki. Sannan ya mika alluran rigakafin kwalara da sauran kayan aikin kiwon lafiyar da ake bukata domin yaki da cutar ga gwamnati da al’ummar Borno, da nufin kai daukin gaggawa,” a cewar sanarwar.

Haka shima, kwamishinan lafiya da taimakon al’ummar jihar, Farfesa Baba Mallam ya tabbatar da hakan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG