Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Yi Ikirarin Kashe Ma'aikatan Agaji Hudu - Kungiyar Agaji


Hukumar bada agaji ta duniya Action Against Hunger, ta ce masu tayar da kayar bayan da suka yi garkuwa da ma’aikatan agaji shida a Arewa maso gabashin Najeriya a watan Yuli, sun yi ikirarin sun kashe mutum hudu daga cikin ma’aikatan.

Hukumar bada agaji ta Action Against Hunger, ta fadi jiya Juma’a cewa wannan ikirari na baya-bayan nan ya sa yawan ma’aikatan da aka kashe ya kai biyar, an kashe mutum na farko a watan Satumba.

Haka kuma, hukumar ta yi kira cikin gaggawa da a saki ma’aikaciyarta Grace, wadda har yanzu ake tsare da ita.

Wata sanarwa da hukumar agajin ta fitar a watan Yuli na cewa “An yi garkuwa da ma’aikaciyar hukumar agaji ta Action Against Hunger da direbobi biyu da kuma wasu ma’aikatan ma’aikatar kiwon lafiya uku, a yayin da suke kan hanyarsu dauke da kayan agajin gaggawa ga mabukata a jihar Borno.

An yi imanin wadanda suka aikata wannan danyen aikin mambobin kungiyar ISIS reshen yammacin Afirka dake alaka da kungiyar Boko Haram.

Hukumar agaji ta Action Against Hunger, ta ce yanzu haka tana bayar da tallafin abinci duk wata ga mutane kimanin dubu 300 a Arewa maso gabashin Najeriya, wadanda basu da wata hanyar samun abinci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG