Wannan ne karo na biyu a cikin abin da bai fi wata daya ba da kungiyar ke yunkurin kai hari a garin na Damaturu.
To sai dai tamkar a lokacin farko, wannan karon ma maharan ba su sami nasara ba, a daidai lokacin da jami’an tsaro suka fitar da sanarwar cewa sun fatattake su, to amma ba su bayar da cikakken bayanin yadda lamarin ya auku ba.
Wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun ce maharan sun faro ne daga garin Babban Gida, shelkwatar karamar hukumar Tarmuwa, duk da yake babu cikakken bayanin ainihin abin da ya faru a garin ya zuwa lokacin hada wannan labarin, to amma ana zargin ‘yan bindigar sun lalata hanyoyin sadarwa na garin, ta yadda ba za a sami labarin abin da ke faruwa ba.
Sardaunan Damaturu Alhaji Bello Arabi, ya bayyana cewa dalilin da ya sa ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka addabi jihar ta Yobe, iri daya ne da na makwabciyar ta jihar Borno.
“Mun gane cewa burinsu shi ne Yobe da Borno suke so su lalata, domin sun san cewa idan suka lalata su to sun sami hanyar shiga su mamaye Arewacin Najeriya gaba daya” in ji Sardaunan na Damaturu.
To sai dai a ra’ayin masanin kimiyyar zamantakewa da halayyar dan Adam, Farfesa Tukur Muhammad Baba na Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi, “wannan ya nuna tababa akan ikirarin da gwamnatin tarayyar kasar ke yi na cewa tana samun nasara a yaki da kungiyar ta Boko Haram”.
Wannan yunkuri na baya-bayan nan ya zo ne ‘yan kwanaki bayan mummunan harin da ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka kai kan matafiya a garin Auno, inda suka kashe mutane fiye da talatin, tare da kona dukiya mai dimbin yawa.
Ga cikakken rahoton Hassan Maina Kaina
Facebook Forum