Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BOKO HARAM: Majalisar Dinkin Duniya Ta Kai Ziyara Kamaru


'yan gudun hijira a kasar Kamaru
'yan gudun hijira a kasar Kamaru

Firai Ministan kuma shugaban gwamnatin kasar Kamaru Phlemon Yang ya karbi bakuncin Ma'taimakin babban magatakardar MDD mai kula da ayyukan jinkai da taimako kayan masarufi na 'yan gudun hijira, Steven O’Bright a ofishinsa dake birnin Yaounde.

Sunyi ganawa ta gaba da gaba ne kan yadda kasar Kamaru take fama da hare haren kungiyar Boko Haram dama tada bama bamai na kunar bakin wake da kungiyar Boko Haram ke yi a arewacin kasar Jamhuriyar Kamaru.

A halin yanzu dai kasar Kamaru ta karbi ‘yan gudun hijira dama da dubu dari da hamsin wadanda suke gujewa hare haren kingiyar Boko Haram, wadanda suke makwabtaka daga kasashen dake makwabtaka da Kamaru, galibi daga arewa maso gabashin Najeriya.

Banda haka kuma, kasar Kamaru na fama da kwararar ‘yan gudun hijira daga kasar Afrika ta tsakiya yankin Bangi kuma ‘yan tawayen Bangi.

Yanzu haka dai akwai kimanin ‘yan gudun hijira dubu dari biyar da suka hada da ‘yan kasar Kamaru da suka rasa matsugunansu sakamakon wadannan tashe tashen hankalin.

Ga rahoton da wakilin Sashen Hausa da Mamahad Awal Garba ya aiki daga birnin Yaounde, kasar Kamaru.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:58 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG