Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birtaniya Ta Bukaci Bayani Daga Rasha Kan Harin Guba


Firayim Ministar Birtaniya Theresa May
Firayim Ministar Birtaniya Theresa May

Fiarayim Ministar Birtaniya Theresa May ta ce kasar Rasha ce ta kai hari cikin kasarsu wanda ya hallaka wani tsohon dan leken asiri Sergei Skipal da diyarsa lamarin da ya sa yanzu an bukaci cikakken bayani daga kasar Rasha cikin kwanaki uku

Firayim Minista Theresa May ta Britaniya ta fada jiya Litinin cewa wata guba mai karfin gaske wadda kasar Rasha ta kirkiro, it ace aka yi amfani da ita a harin da aka kai kan wani tsohon dan leken asirin Rasha, Sergei Skripal, kuma gwamnatinta ta cimma shawarar cewa a bisa dukkan alamu, kasar Rasha ce ta kai harin.

May ta fadawa majalisar wakilan Britaniya cewa abubuwa guda biyu ne kawai zasu iya faruwa a harin da aka kai kan Skripal da diyarsa Yulia, aka same su kwance a some a cikin wani ghari na kudancin britaniya a ranar 4 ga watan nan na Maris.

Ta ce, “ko dai gwamnatin Rasha ce ta kai harin nan kai tsaye a kan kasarmu, ko kuma dai gwamnatin Rasha ta yi sakacin barin wannan mummunar guba ta yadda har ta fada hannun wasu.”

Britaniya ta ba gwamnatin Rasha wa’adin kwanaki biyu da ta yi mata bayani.

Firayim minister ta Britaniya ta ce wannan sinadarin guba mai tsananin karfi da aka yi amfani da ita, it ace Novichok, wadda ke nufin Sabuwar Shigowa da harshen Rashanci.

Jim kadan kafin ta yi wannan jawabi, shugaba Vladimir Putin na Rasha yayi watsi da ikirarin cewa Rasha tana da hannu a wannan lamari na Skripal, wanda kanar ne a hukumar leken asirin sojoji ta Rasha, amma a boye yana aikin leken asiri ne ma hukumar leken asirin Britaniya ta MI6.

Gidan telebijin na Rasha sun a dora laifin sanya ma Skripal guba a kan Britaniya, suna ikirarin cewa Britaniya na kokarin janyo kin jinin Rasha ne domin haddasa yanayin da za a kauracewa gasar cin kofin kwallon kafar duniya da za a yi a Rasha nan da ‘yan watanni.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG