Sakataren harkokin wajen Burtaniya, ya yi kira ga kasashen kawance na asali na yammacin Duniya, da su zo a hada kai domin tunkarar abin da ya kira “muggan dabi’un,” da Rasha ke nunawa, yana mai bayyana kwarin gwuiwar cewa, Amurka, karkashin shugabancin Donald Trump, za ta jagoranci wannan tafiya.
Sakataren harkokin wajen na Burtaniya, Jeremy Hunt, ya fadawa wani taro a Washington cewa, yana da muhimmanci, Amurka da Burtaniya da kungiyar Tarayyar Turai, su zama tsintsiya madaurinki daya wajen tunkarar halayen shugaban Rasha, Vladmir Putin, na kai munanan hare-haren da suka take dokokin kasa da kasa da aka dade ana amfani da su.
Gabanin ya gana da mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence da sakataren harkokin wajen kasar, Mike Pompeo, a jiya Talata, Hunt ya kara da cewa, “wadanda ba sa tare da muradunmu, su kwan da sanin cewa, akwai mummunan sakamako da zai biyo baya, idan har suka tsallake shingen da aka gindaya musu, suka mamaye wasu yankuna, ko suka yi amfani da wani makami da aka haramta, ko kuma suka dukufa wajen kai hare-hare akan rumbun bayanan internet.
Facebook Forum