Kiran ya biyo bayan rugujewar wani bene mai hawa daya da shaguna a garin Bukur dake karamar hukumar Jos ta Kudu a Jahar Filato.
Ginin wanda aka yi a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu, an kara dora masa hawa daya aka kuma fadada shi zuwa shaguna da ofisoshi.
Jami’in hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, shiyyar Arewa ta tsakiya, Nuruddeen Musa yace babu rai da ya salwanta sai dai ya danganta rushewar ginin da rashin yin amfani da ingantattun kayan aiki.
‘Wan mai gidan, Bitrus Gyang Pam yace dan’uwansa Musa Bitrus Pam bai ga wata alamar rushewar ginin ba sai daren da lamarin ya auku, inda ya yi kira ga hukumomi da su taimaka don farfado da kasuwancin da mutane fiye da goma ke amfana.
Tun farko hukumar kula da yanayi ta kasa ta yi hasashen yawaitan ruwan sama a bana da ka iya yin barna, don haka ta shawarci al’umma da su kula da muhallinsu don kaucewa ibtila’i.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: