Kwararru a fannin tsaro a Najeriya na ci gaba da nuna muhimmancin amfani da bayanan sirri, wajen shawo kan matsalar hare-haren ‘yan bindiga a yankunan arewa maso yammacin kasar.
Kiran na zuwa ne bayan kisan gillar da 'yan bindiga suka yi wa wasu manoma a yankin karamar Hukumar Batsari da ke jihar Katsina a ranar Litinin.
“A kowace karamar hukuma, a samu mutane da za su rika kawo bayanai. Nawa ne gwamnati za ta kashe wajen biyan mutum 50 ko 100 suna ba da bayanan da za dakile wadannan ‘yan ta’adda?” In ji tsohon babban kwamanda a rundunar sojojin Najeriya, Manjo Janar Junaidu Bindawa.
Kalaman da masanan ke yi na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa dakarun Najeriya na samun nasara a farmakin da suke kai wa a dazukan da 'yan bindigar ke buya.
Rundunar sojojin saman Najeriya ta kaddamar da wani sabon farmaki mai taken
"Operation Accord” da ke karkashin Farmakin “Operation Hadarin Daji” a jihar Sokoto don kawo karshen ta'asar ‘yan bindiga dadin.
Babban Hafsan Hafsoshin mayakan saman Najeriya, Air Marshall Sadique Abubakar ya ce wannan farmaki tuni ya aike da dimbin ‘yan bindiga barzahu tare da rugurguza da dama daga sansanoninsu.
Ya ce za a ci gaba da kai farmakin ne ba dare ba rana har sai an cimma samar da zaman lafiya a jihar.
Daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu a yankin arewa maso yammacin Najeriya cikin ‘yan shekarun bayan nan sanadiyyar hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa da kuma masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
Facebook Forum