Mataimakin darektar kungiyar Keiji Fukuda yace za’a dauki karin watanni hudu nan gaba kafin a shawo kan cutar, wacce tuni ta halaka mutane dari da goma.
Har yanzu dai bullar anobar cutar yafi tsanani a kasar Guinea inda ake zato ko aka tabbatar da mutane dari da hamsin da bakwai sun kamu da cutar ta Ebola.
Kasar Laberiya makwapciyar kasar, kuma an sami tabbaci ko zaton mutane 21 sun kamu da cutar.
A wani taron manema labarai jiya Talata a birnin Geneva, Fukuda yace barkewar cutar na yanzu ya zame kalubale na musamman domin cutar ta bazu a wurare masu yawa.