A tattaunawar da yayi da Sashen Hausa na muryar Amurka, mataimakin gwamnan yace abubuwan da ya ganewa idanunsa da ya ziyarci wuraren da abin ya faru sun tabbatar masa da wannan hasashen, kuma ya kamanta wannan harin da wani wanda aka kai a garin Gwaram kwanakin baya.
Yace wadannan 'yan bindigar sun yi ta harbi a iska, suka kori mutanen gari, suka dasa bam karkashin wata mota jmai sulke ta 'yan sanda dake gadi a bakin kofar gidan tsohon sufeto-janar na 'yan sanda, Hafiz Ringim, suka kai farmaki kan ofishin 'yan sanda na garin, sannan suka killace suka kuma fasa bankin Unity.
Yace wadanda aka kashe su biyar sun hada da 'yan sanda uku da kuma masu gadi guda biyu na wannan banki.