Hakan kuwa na da alaka da yadda kalubalen tsaro yaki ci yaki cinyewa da kuma kamfan ruwan sama.
Wannan ja’iba dai da Bankin na Duniya ya hararo abu ne da ya shafi wasu kasashe a tsakiya da yammacin Afirka.
Kasashen Najeriya, Mali, Tchadi da Nijar nan ake tunanin inda al’amura ka iya tabarbarewa sosai ganin dukkanninsu na fama da matsalar tsaro iri iri.
A dai wadannan kasashe kusan kashi biyu na irin abincin da ake Nomawa ne aka gaza sanarwa sakamakon kara lalacewar harkar ta tsaro.
Yanzu haka dai binciken da Wakilinmu ya gudanar ya nuna tuni galibin jihohin da Bankin Duniya ya Amhata ke ta fama da taron matsalolin rayuwa a sakamakon aika aikar yan bindiga
Yanzu ta kai jallin da kanzo ke kam shin dan goma a ire iren wadannan yankuna
Wani mai bibiyar lamurran tsaro, Basharu Isa ya ce tuni dama su suna sane cewa hakan zai kasance musamman in aka yi la’akari da halin da ake ciki.
A bangare daya kuma, rundunar sojin Najeriya ta ce tana iya bakin kokarinta wajen ganin ta shawo kan kalubalen tsaron don kasar su sami sukunin gudanar da harkokin rayuwa na yau da kullum, kamar yadda Janar Edward Buba na hedkwatar rundunar sojin kasar ya shaidawa VOA Hausa.
Bankin Duniya Ya Yi Hasashen Kara Rincabewar Al’amura A Yankunan Wasu Jihohin Arewacin Najeriya.
Abuja, Nigeria —
Dandalin Mu Tattauna