A jiya Alhamis ne Babban Bankin duniya, da kuma Asusun bada lamuni na duniya wato IMF suka bada sanarwar cewa kasar Somaliya ta cancanci a yafe mata basussu kanta, biyo bayan sauye sauye a fannin tattalin arziki da ma’aikatu da hukumomi suka yi.
Ana bin Somaliya bashin da masu bada bashi na kasashen waje da aka kiyasta ya fi sama da dalar Amurka biliyan biyar ($5B). A cikin basussukan da ake bin Somaliya babba shine na dala biliyan daya ($1B) da Amurka take binta.
A cikin wata sanarwa da aka fitar bayan da kwamitin koli suka tattauna a ranar 12 da 13 ga watan Fabrairu, don su duba cancantar Somaliya, hukumomin harkokin kudin masu karfi a duniya guda biyu sun goyi bayan Somaliya da a yafe mata bashinta a karkashin shirin kasashen matalauta masu tsananin bashi na (HIPC a takaice).
Kasashen da suka cancanta na wannan shirin sun yi alkawarin inganta tattalin arziki da kudade da kuma rage yawan talauci.an kwashe shekaru da dama, Somaliya tana karkashin shirin kulawar ma’aikatan IMF da ya taimakawa Somaliya inganta hanyoyin karbar haraji da bin diddgig na bayanan kudade na gwamnati.
Facebook Forum