Sakataren yace abu guda da suka tattauna kawai, shine batun jami'an jam'iyyar wadanda hukumar zabe ta Najeriya ta ayyana cewa ba a zabe su bisa ka'ida ba, kuma Bamanga Tukur ba ya cikin wadannan mutanen.
Ya kalubalanci masu cewa a cire Bamanga Tukur, yana mai fadin cewa ai idan akwai masu neman ya sauka, sai su zo gaban taro irin wannan su fadi haka. Yace babu wata hujja da wasu mutanen dabam zasu matsa musu lamba a kan su kori shugabansu.
Haka kuma yayi watsi da ikirarin cewa akwai wasu gwamnonin jam'iyyar PDP wadanda suka lashi takobin sai sun ga bayan shi Bamanga Tukur, inda yace wani ya fito yace yana son Bamanga ya sauka wani abu ne dabam, bin ka'ida kuma dabam ne. Yace majalisarsu ta bi ka'ida kan wannan batun.
Ga bayanin Sanata Walid Jibrin a tattaunawarsu da Nasiru Adamu el-Hikaya.