Wadannan tashin boma boman dai kusan shine karo na bakwai ko kuma na shida a cewar kwamishinan ‘yan sandan jihar a cikin mako guda. Wanda hakan yasa mutanen dake cikin garin Maidugurin fara tofa albarkacin bakinsu akai kan dawowar tashin bama baman a garin.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mr. Damian Chukwu, yace yau da asuba ne da missalin karfe Hudu aka samu tashin bam din na farko a wata unguwa da ake kira Jiddari, kusa da wata kotu inda ake bincikar ababen hawa.
Biyu daga cikin ‘yan kunar bakin waken mata ne yayin da ‘dayan ya kasance namiji. Kwamishinan yace ‘daya daga cikin matan tayi kokarin kunce bom din daga jikinta yayin da namijin ya amsa a kokarin da yake na jigida da bom din, bom din ya tashi ya kashe shi ya kuma kashe ‘daya yarinyar da suke tare. Sa’ar da akayi itace macen da ta cire bom din daga jikinta bom din bai hallaka ta ba.
Jami’an ‘yan sanda dai na samun bayanai daga macen data rayu kafin daga bisani su mika ta zuwa ga jami’an soja don ci gaba da bincike.
Da missalin karfe Takwas da rabi ne na safiyar yau ne kuma kwamishinan yace ya samu wani labarin tashin wasu boma bomai biyu akan titin garin Maiduguri zuwa garin Gamboru. Daya daga cikin ‘yan kunar bakin waken na niyyar kokarin kutsawa cikin garejin da ake kira Muna Garage, bom din ya tashi inda ya hallaka dan kunar bakin waken shi kadai.
Shi kuma bom din na uku ya tashi a lokacin da wani dan kunar bakin wake yayi kokarin shiga cikin gari, inda aka hanashi cikin hakan ne ya tayar da bom din dake jikinsa, wanda ya hallaka shi ya kuma hallaka wasu ma’aikatan sa kai na kungiyar Civilian JTF guda biyu.
Sakamakon tashin boma boman dai yanzu haka dai ana da adadin mutane Shida da suka mutu ciki harda ‘yan kunar bakin waken. Hukumar ‘yan sandan jihar dai sun hana duk wani taro ko zanga zanga da aka shirya yi a yau Juma’a.
Domin karin bayani.