Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bacci Ni'ima ga Rayuwa Mai-Nagarta Tun Yarinta


Rashin Bacci da Makaranta
Rashin Bacci da Makaranta

Cibiyar dakile cututtuka ta Amurka, ta wallafar da wani rahoto da ke nuni da cewar, lokkuttan da yara ‘yan firamari da sakandire ke zuwa makaranta da sanyin sassafiya na shafar lafiyar su!

Wasu bincike da aka gudanar a baya da suke nuni da cewar, lallai akwai bukatar yara kanana su samu bacci a kowane dare, wanda ba zai gaza awowi takwas ba, samun wanna isashen bacin, zai taimaka ma kwakwalwarsu wajen fahimtar karatu da kuma yadda zasu gudanar da rayuwar su a kowace rana.

Babbar matsala da yara ‘yan firamari ko sakandire kan fuskan ta a nan kasar Amurka, ita ce yadda suke tafiya makaranta tun da sanyin safiya, wanda hakan kan zamo dalilin rashin samun wadataccen bacci gare su.

A tabakin marubuciyar wanna rahoto Anne Wheaton, kimanin dalibai biyu cikin uku suke samun matsalar rashin bacci, wanda yake kasa da awa takwas 8 a rana.

Don haka wanna rahoto na bada shawara ga iyaye da yara matasa, da su kokarta wajen ganin sun samu wadataccen bacci a kowane dare, wanda zai taimaka ma kwakwalwa da jikinsu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG