An aika da ma’aikatan ceto don nemo wadanda abin ya hallaka da kuma wadanda su ka samu tsira bayan “an samu bayanai game da gano gawarwakin bakin hauren da suka mutu a hatsarin jirgin, in ji ‘yan sandan kan iyaka.
"Kawo yanzu ba mu da wani bayani game da wadanda suka tsira da kyar" ko kuma kasashen asali na wadanda suka hallaka, kamar yadda wata mai magana da yawun hukumar kan iyaka ta shaidawa AFP.
Ta kara da cewa "Har ila yau, ba mu da tabbacin adadin mutanen da ke cikin jirgin.
Dubban 'yan ciranin ‘yan Kudancin Amurka, musamman 'yan kasar Venezuela ne ke bi ta kasar Panama, hanyar da ke cike da hadari a arewacin kan iyakar Amurka.
Yawancinsu suna shiga ƙasar ta cikin dajin Darien da ƙafa daga Colombia, sannan su ci gaba zuwa Amurka ta tsakiya da Mexico.
Dandalin Mu Tattauna