Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu tabbas gameda harkokin siyasar kasar Yemen

Wasu 'yan kasar Yemen, suke zanga zangar a birnin Sana;a domin goyon bayan yan tawayen Houthi
Wasu 'yan kasar Yemen, suke zanga zangar a birnin Sana;a domin goyon bayan yan tawayen Houthi

A jiya Juma'a babu tabbas gameda makomar harkokin siyasar kasar Yamal, a yayinda aka bada rahoton cewa, gobe Lahadi idan Allah ya kaimu Majalisar dokokin kasar zata yanke shawarar au tayi na'am da murabus din shugaban kasar AbdRabbuh Masur Hadi yayi ko kuma a'a.

A ranar Alhamis, shugaba Hadi da Prime Ministan kasar Khalid Bahah da Majalisar Ministocinsa suka mika takardunsu ta yin murabus, kwanaki bayan da 'yan yakin san kan Houthi suka yiwa muhimman gine gine gwamnati a baban birnin kasar kawanya, suka kuma bukaci a aiwatar da wasu sauye sauye da daftarin tsarin mulkin kasar.
A yayinda yake misali da bayani da Prime Minista kasar yasa a shafinsa na twitter a yanar gizo, kamfanin dilancin labarun Reuters ya ambace shi yana fadin cewa gwamnatin kasar bata son ta sa hannu a harkokin siyasar da basu da ma'ana.
Jiya Juma'a aka yi gangamin goyon baya da rashin goyon bayan kungiyar Houthi a wasu biranen kasar, to amma rahotanin da suke fitowa daga baban birnin kasar sunce al'amurra sun lafa.
A yayinda yake magana daga birnin Sana'a a jiya Juma'a kuma, wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Yamal Jamal Benomar yayi kira ga dukkan bangarorin kasar da su ci gaba da tuntunbar juna da yin shawarwari da zasu sa a kula yarjejeniya akan yadda za'a samu mafita daga rikicin da kasar ke fama da ita a yanzu.
Tunda farko Mr Benomar yace hanyar kawai da za'a bi a magance rikicin siyasar kasar, shine idan kungiyoyi masu gaba ko hamaiya da juna sun mutunta yarjeniyoyin da aka kula a baya, da suka tanadi raba mukamai da kuma kawo karshen tarzoma a kasar.

XS
SM
MD
LG