Muryar Amurka ta gudanar da bincike a kasuwar dabbobi ta 3030 a unguwar Bodija Ibadan, inda ta zanta da wasu masu sayar da dabbobin da kuma masu kai dabbobin kasuwar.
Masu sayar da raguna dai sun koka game da rashin samun ciniki, yayin da suma masu zuwa sayen ragunan sallah ke kokawa game da tsadar dabbobi idan aka kwatanta ta da shekarar da ta gabata.
A cewar Alhaji Habu, wani da ya kawo raguna kasuwar 3030 daga Maiduguri, ya ce ga yanayin kasuwar bana ta fi bara tsada.
Shi kuma Alhaji Kodri, wanda yazo kasuwar domin sayan raguna ya koka ga yadda farashin dabbobin yayi tashin gwauron zabi.
Haka kuma wakilin Muryar Amurka ya zagaya bangaren masu sayar da kayan miya domin jin yadda kasuwar ke tafiya. Wasu daga cikin ‘yan kasuwar sun nuna cewa bana kasuwar ba kamar yadda akayi tsammaninta ba.
Mafi yawan mutane da aka zanta da su a kasuwar sun bayyana cewa kayayyaki sun yi tsada.
Domin karin bayani saurari rahotan Hasssan Umaru Tambuwal.
Facebook Forum