Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kwastan Shiyar Legas Ta Kama Tabar Wiwi da Kudinta Ya Kai N72m


Tabar wiwi da wasu kayan da hukumar kwastn ta kama
Tabar wiwi da wasu kayan da hukumar kwastn ta kama

Hukumar kwastan dake kula da jihohin Legas da Ogun ta kama manyan motoci cike da tabar wiwi da kudinta ya kai N72m tare da wasu kayan da suka hada da motocin alfarma.

Hukumar kwastan mai kula da jihohin Legas da Ogun ta kama tabar wiwi mai nauyin kilogram 1590 da kudinsu suka haura N72m makonni ukun da suka gabata.

Kamun na zuwa ne bayan kama buhunan shinkafa 1237 wadanda aka ce gurbatattu ne da kudinsu ya kai N15m da aka shigo dasu ta kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin.

Shugaban hukumar kwastan mai kula da yankin Alhaji Muhammad Uba Garba shi ya bayyana hakan a firar da yayi da manema labarai.

Yana mai cewa sun kama kaya da dama da suka hada da motocin alfarma 27 tare da kayayyaki guda 54 da suka hada da shinkafa da magunguna da ganye da tsoffin tayoyi da sauran kayan kasuwa. A cikin kayan akwai wadanda doka tace a shigo dasu akwai kuma wadanda doka ta hana amma idan mutum ya boye wadanda doka ta hana aka kuma gano to duka kayan za'a kwace gaba daya. Irin wadanna kayan kudinsu sun kai N700m da 'yan kai.

Akan batun sumoga Injiniya Awal Ibrahim na kungiyar masu kananan masana'antu ya ce hana shigowa da kaya nada kyau. Ya yi misali da kasar China da ke hana shigowar kaya domin kare nata 'yan kasar domin su samu dogaro ga kansu.

Har wayau hukumar ta kama wasu motoci 64 su ma na alfarma da kudinsu ya kai N1.5bn.

Irin motocin da hukumar kwastan ta kama
Irin motocin da hukumar kwastan ta kama

Yanzu hukumar ta tabbatar da koran jami'anta guda hudu wadanda ake zargi suna da hannu wajen shigo da manyan makamai 661 ta tashar Tin Can

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG