Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata Da Miji Da 'Ya'yansu Sun Kai Harin Kunar Bakin Wake A Indonesiya


Harin da aka kai wata majami'a a Indonesiya
Harin da aka kai wata majami'a a Indonesiya

Kungiyoyin Musulmi da na Kirista sun yi Allah wadai da hare-haren da aka kai a wasu Majami'u a kasar Indonesiya.

‘Yan sanda a kasar Indonesia na zargin wani iyali mai kunshe da yara kanana, da kai harin kunar bakin wake a majami’u a yau dinnan Lahadi, inda mutane akalla 11 su ka mutu baya ga wasu 41 da su ka ji raunuka, wasu ma a cikin birnin Surabaya.

Tuni kungiyar ISIS ta dau alhakin wadannan fashe-fashe a birni na biyu a girma a kasar.

Sufeton ‘yan sandan kasar Tito Karnavian ya ce maharani sun hada da uwa da uba, da ‘yan mata biyu masu shekaru 9 da 12 da kuma kananan yara maza su ma biyu. Ya ce iyalin na da alaka da wata kungiya mai alaka da ISIS mai suna Jama’a Ansharut Daulah.

Tuni dai kungiyoyin Musulmi da na Kirista na kasar ta Indonesia su ka yi Allah wadai da hare-haren, sannan su ka fitar da wata takardar bayani mai cewa, “Baba wani addini a duniyar nan da ya halatta tashin hankali don cimma burinsa.”

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG