Wani babban jami’in diflomasiyyar Amurka a Ukraine, ya fadawa jami’an majalisar wakilan kasar cewa, an sanar da shi cewa Fadar gwamnatin Amurka ta White House, ba za ta saki wasu kudaden tallafin kayayyakin soji ga kasar ta Ukraine ba, har sai ita Ukraine din ta fito fili ta yi alkawarin cewa za ta binciki ‘yan jam’iyyar Democrat da iyalan gidan tsohon mataimakin shugaban Amurka Joe Biden.
Mukaddashin jakadan Amurka a kasar ta Ukraine, Ambasada William B. Taylor, ya bayyana hakan ne yayin da yake ba da shaida cikin sirri a zaman binciken da majalisar ke yi, wanda ke duba yiwuwar tsige Shugaba Trump, shaidar da ta yi karo da ikrarin da Shugaba Trump ya yi cewa, babu batun cude-ni-in-cude-ka a tsakaninsa da Ukraine.
Taylor ya kara jaddada matsayarsa cewa, “babu hankali” a matakin da aka dauka na rike kudaden tallafin, wanda Ukraine ke matukar bukata.
Shi dai Shugaba Trump ya musanta aikata ba daidai ba a zarginsa da ake yi na cewa ya nemi Ukraine ta binciki abokanan hamayyarsa musamman Hunter Biden, dan tsohon mataimakin shugaban Amurka kan rawar da ya taka a wani kamfani da ya yi aiki da shi mai suna Burisma a kasar ta Ukraine.
Facebook Forum