Babban Hafsan tsaron Najeriya Janar Lucky Irabo ya kai ziyara jihar Filato da ke tsakiyar arewacin Najeriya a wani mataki na tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a jihar.
Yayin ziyarar tasa, Janar Irabor ya fara yada zango ne a fadar gwamnati, kamar yadda wata sanarwa dauke da sa hannun Darektan yada labaran jihar Dr. Makut Simon Macham ta nuna.
Irabor ya fadawa Gwamna Simon Lalong cewa shugaban kasa ya ba su umarnin su yi duk abin da za su iya wajen zakulo wadanda suka ta da husuma don a hukukta su tare da tabbatar da cewa hakan bai sake faruwa ba.
A cewar sanarwar ta Macham, Irabor ya ce “zaman lafiya na samuwa ne idan al’umomi suka amince su zauna lafiya tare da fallasa ayyukan baragurbin da ke cikinsu.”
Yayin nasa jawabin, gwamna Lalong ya fadawa Janar Irabor cewa, zaman lafiya ya dawo jihar ta Filato amma akwaia dabbaka shi.
“Akwai bukatar a kara mayar da hankali wajen tabbatar da doka da oda da kuma sake gina tubalan zaman lafiya,” a tsakanin al’uma. In ji Lalong.
A ‘yan kwanakin Jos, babban birnin jihar ya fuskanci rigingimun da suka yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi da dama, tun bayan kashe wasu matafiya da wasu matasa suka yi a yankin Rukuba Road da ke kusa da Gada Biyu.
Kwanakin kadan bayan wannan hari akan matafiyan, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun abkawa al’umar yankin Yelwan Zangam a Jos ta Arewan, inda a nan ma aka yi asarar rayuka da dukiyoyi.
Birnin na Jos wanda ya sha fama da rigingimun da ake alakantawa da kabilanci da addini, ya jima rabon da ya fuskanci wata tarzoma a ‘yan shekarun baya-bayan nan.
Ko da yake, akwai daidaikun rigingimu da kan taso a wasu kananan hukumomin jihar da ke kewaye da birnin na Jos.
Yanzu haka birnin na cikin dokar hana fita wacce ke farawa daga 6 na yamma zuwa 6 na safe.
Gabanin sassauta dokar zuwa wannan mataki, al'umar birnin ta kwashe kusan mako guda karkashin dokar hana fita ta sa'a 24.
Saurari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji: