Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jihar Borno Wani Ya Kori 'Yan Gudun Hijira daga Filinsa Saboda Ya Kara Kudin Haya


Irin rumfunan kara da 'yan gudun hijiran ke ciki ke nan da suka kafa a filin da suke.
Irin rumfunan kara da 'yan gudun hijiran ke ciki ke nan da suka kafa a filin da suke.

Kowane dan gudun hijira na biyan N1000 a matsayin kudin haya kowane wata bisa dan filin da ya kafa rumfarsa kafin mai filin ya kara kudin hayar zuwa N2000 wata duk da cewa yawancinsu ba wani aiki suke yi ba.

Korar da mai filin ya yi masu ya sa sun sake fadawa cikin wani halin kakanikayi saboda dukanasu mutane ne da suka baro duk abun da suke dashi baya.

'Yan gudun hijiran sun fito ne daga garuruwan da 'yan Boko Haram suka karbe kafin a sake kwatosu. Amma duk da sake kwato garuruwan dole ne a sake ginasu kafin su iya komawa.

Yan gudun hijira
Yan gudun hijira

Yanzu dai 'yan gudun hijiran sun fice daga filin domin babu wani ginannen gida ciki. Su ne suka gina rumfunan kara su samu matsuguni amma kuma tare da biyan kudin haya.

Yanzu suna wata anguwa da ake kira Shuwari Madinatu inda suka sake gina rumfuna domin samun wurin kwana kuma mafi yawansu mata ne tare da 'ya'yansu. Wani bawan Allah ne ya basu nashi filin.

Wakilin Muryar Amurka da ya zagaya inda 'yan gudun hijiran suke sun fada masa cewa basa samun taimako daga koina. Hatta ruwan sha sai sun fita su roka kafin su samu wanda zasu sha.

Yanzu kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa domin sake gina arewa maso gabas ya gano wadannan 'yan gudun hijiran kuma ya soma taimaka masu da abinci bayan da wakilin Muryar Amurka ya jawo hankalin mahukunta kan sansanin na wadannan 'yan gudun hijiran

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:08 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG