Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ruwa Abokin Aiki, Don Kuwa Yana Maganin Cututtuka Da Dama!


Ruwa
Ruwa

Shan ruwa da ya kai adadin lita biyu, nada matukar mahinmanci ga rayuwar dan’adam a kullun. Duk dai da cewar yanayin jikin mutun, da iya irin aikin da yake aikatawa a yini, na kara bayyanar da yawan bukatar da jikin mutun yake da shi wajen shan ruwa.

Yana da matukar muhimanci mutun ya sha ruwa da suka kai wannan adadin, don tahaka ne wasu cuttutuka ba zasu samu wajen zama a cikin jikin mutun ba, idan mutun na shan ruwa yadda ya kamata a yini. A duk lokacin da wasu sassan jikin mutun suka bukaci ruwa, musamman idan mutun yayi aikin motsa jiki, to yana da kyau mutun ya inganta jikin shi da wadataccen ruwa.

A wani bincike da wata malamar kiwon lafiya ta gudanar Jessica Fishman, tace akwai bukatar mata su sha ruwa da ya kai kimanin kofi goma sha daya 11 a yini, sai ta kara da cewar, abun nufi ba wai mace ta dauki kofi tai ta shan ruwa ba, abun nufi shi ne ta sha ruwa, kana ta sha wasu nau’o’in abinci da suke dauke da ruwa.

Idan za’a gwada adadin yawan ruwan da mutun ya sha sai aga cewar, ya kai kimanin yawan kofi goma sha dayan da ake magana. Koda kuwa mutun yana jin yunwa kada ya bari yawan ruwan dake cikin jikin shi ya gaza adadin da ake bukata mutun ya samu a kowane lokaci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG