Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lauyan Amirka na musaman ya tattara mutane da zasu binciken zargin da ake yiwa kasar Rasha


Robert Myeller
Robert Myeller

Lauyan gwamnatin Amirka na musamman Robert Mueller ya tattara mutane da zasu binciki zargin karya doka domi tantance ko a gudanar da shari'ar ko kuma a'a

Mujallar The Wall Street Journal ta rubuta labarin cewar lauya na musamman Robert Mueller ya tattara mutane da zasu binciki zargin karya doka, domin tantance ko shedun da aka samu, sun wadatar a gudanar da shari'a ko kuma a.a Daukan wannan mataki yana nufin za'a gudanar da bincike a kan batun katsalandar da ake zargin Rasha da aikatawa a zaben shugaban kasa a shekarar 2016 na kara girma.

Masu bincike da masu shigar da kara sun yi amfani da zaman mutanen na musamman, wurin tattance shaida da yiwa wadanda suka baiyana gabansu tambayoyin sanin kwakwaf, da kuma samacin samun takardu ko kuma bayanan kotu domin tantance ko an aikata laifi. Idan har aka gano an aikata laifi, mataki ne mai muhimmanci ga kowane irin bincike..

Mueller da lauyoyinsa suna bincike ne a kan yuwar hadin baki tsakanin Rasha da kwamitin yakin neman zaben Trump.

To amma kuma a wani jawabin daya gabatar na bijirewa da yammacin jiya Alhamis, shugaba Donald Trump ya kira labarai a kan kulla alaka tsakainin kwamitin kempensa da kasar Rasha a matsayin kage dake ba abokan adawarsa jin dadi, bayan sun sha kaye a zaben da aka yi bara.

Kalaman na shugaban sun zo a lokacin da masu pashin baki da masu sharhi a kan harkokin siyasa suke nanata muhimmanci da babban lauyan yaba wannan batu na kafa kwamtin masu taimakawa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG