Fim din Baahubali, ya kafa tarihi a Bollywood, ya zama fim na farko daya sami kudaden shiga fiye da dalar Amurka miliyan dari biyu da arba’in $240 a cikin dan kankanin lokaci.
Yanzu haka wadanda suka shirya fim din na Baahubali, na shirye shiryen zuwa da fim din kasar China, a karshe wata mai zuwa kuma ana harsashen cewa fim din zai doke irin rawar da fim din Sultan da Dangal suka taka a kasar ta China, ganin irin kasuwar da fim din yayi a kasar Indiya inda ya takar rawar a zo a gani da kuma samun kudaden da babu wani fim din da ya taba samu a dan takaitacen lokaci a tarihin Bollywood.
A cewar masu shirin fim din za a nuna fim din a gidajen kallo har dubu shida 6,000, kuma za suyi duk abinda ya dace su ga cewa fim din ya yagi rabonsa a kasar China.
Domin karawa fim din ta goma shi za a nuna fim din ne a cikin harshen Mandarin wanda shine harshen da ake amfani dashi a kasar ta China, wadannan mahimman abuwa biyu daga dukkan alamu zasu taimaka fim din yayi kasuwa a kasar ta China.
Kamfanin E-Star Entertainment ne zai nuna fim din, masu harsashen kuma na ganin cewa fim din zai samu dala miliyan $320M a kasar China.
A can baya dai fim din Dangal ya sami fiye da dalar Amurka miliyan $163M a watan da ya gabata kuma a nuna fim din a gidajen kallo dubu bakwai ne 7,000, shin Baahubali zai iya doke Dangal kuwa a kasance da Dandalinvoa domin samu Labarai yadda ta kaya.
Facebook Forum