Wata mata mai shekaru arba’in da uku da haihuwa ta bada kyautar mahaifarta ga ‘yarta matashiya mai shekaru ashirin da daya da haihuwa wace aka haifa babu mahaifa.
Kamar yadda jaridar Hindustan, ta kasar Indiya ta ruwaito, wannan shine karon farko da za a yi dashen mahaifa a kasar Indiya. mahaifiyar matashiyar ta amince da a cire mahaifatar a dasawa ‘yar ta domin itama ta samun damar haihuwa kamar sauran mata.
Dr. Shailesh Puntambekar, ne ya jagoranci wanna tiyatar a Pune dake kudancin kasar Indiya a Asibitin Galaxy Care.
Jim kadan baya da aka kammala tiyatar wanda aka kwashe awowi tara da rabi ana gudanarwa Dr. Puntambekar, yace matashiyar ta na lafiya.duk da yake tiyatar na da wahala.
Ya kara da cewa zata jira shekara daya kafin tayi kokarin son daukar ciki wanda shima cikin dasa mata kwai za a yi.
Wani kwararran likatan mata Dr. Mats Brannstrom, na jami'ar Gothenburg dake kasar Sweden, yace kawo yanzu an haifi yara shida ta hanyar dashen mahaifa.