Amurka ta gargadi Iran, inda ta ce kada ta dauki dakatar da harin da shugaba Trump ya ba da umurnin a yi, a matsayin “ragwanci.”
Amurka dai ta shirya kai harin martani akan Iran, bayan da ta kakkabo wani jirgin Amurka mara matuki a kusa da mashigin Hormuz.
Yayin wata ziyarar da ya kai a Birnin Kudus gabanin ya gana da Firai Ministan Isra’ila Benjyamin Netanyahu, Mai ba da shawara kan harkokin tsaron Amurka, John Bolton, ya ce kada ita Iran din ko wata kasa da ke yi wa Amurka kallon hadarin kaji, su dauka rashin zuciya ne ya sa Amurka ba ta mayar da martani ba, domin ta yi amfani ne da “sanin ya kamata.”
Gargadin da Bolton ya yi, na zuwa ne sa’o’i bayan da Shugaba Trump, ba tare da ba da wani cikakken bayani ba, ya ce zai kara wasu sabbin takunkumi akan Iran a ranar Litinin.
A ranar Asabar Trump ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter, inda ya jaddada cewa, babu yadda za a yi Iran ta mallaki nukiliya, yana mai cewa, za a cire mata takunkuman da aka saka mata da zaran ta yi abin da ya kamata.