Ministan harkokin wajen Iran, Ali Akbar Salehi ya kira kazafin dake cewa shirin jawo hadarin jirgin kasan na da alaqa da Iran a matsayin “karya, kuma wani abu da hankali ba zai dauka ba.”
Tun dai a shekara ta 2012 ne Iran da Canada suka daina mu’amalar diflomasiyya da juna.
Za’a saurari karben belin Chiheb Esseghaier mai shekaru 30 da Raed Jaser mai shekaru 35 ranar Talata a can birnin na Toronto.
Duk da cewa masu bincike sunce mutanen guda biyu suna da niyya, da kuma kayan aikin kai wannan hari, sunce basu da wata barazana ga mutane, ma’aikatan kamfanin jirgin kasan da fasenjoji da ma jiragen da taragonsu.
Hukumar Jami’an tsaro ta Royal Canadian Mounted Police ta ce tayi nasarar kama mutanen guda biyu da taimakon jami’an Amurka. Shi dai wannan shiri na kai harin bashi da wata alaqa da harin da aka kai a birnin Boston a makon da wuce a nan Amurka.