Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Na Goyon Bayan Mulkin Karba-Karba, Dan Najeriya Kawai - Babangida


Janar Ibrahim Babangida mai ritaya.
Janar Ibrahim Babangida mai ritaya.

A yayin da jam’iyyun siyasa a Najeriya suka soma shirye-shiryen tsayar da ‘yan takara domin tunkarar babban zaben shekara ta 2023, tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badmasi Babangida ya yi kira ga ‘yan siyasa da su sanya kasar a gaba, fiye da bukatunsu na siyasa.

A wata zantawa da Muryar Amurka, Babangida ya ce zaman lafiya da hadin kan Najeriya, shi ne babban muhimmin al’amari da idan babu shi, to ba wata nasara da za’a samu a zabe.

“Fatarmu ga ‘yan siyasa shi ne ayi zabe lafiya ba tare da tashin hankali ba” in ji Janar Babangida mai murabus.

Ya kara da cewa “duk abin da zai kawo tashin hankali a lokacin zaben nan su yi kokari kar su shiga ciki.”

Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Janar Ibrahim Babangida.
Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Janar Ibrahim Babangida.

Tsohon shugaban kasar ya ce yanzu haka ana fuskantar kalubalen tsaro a yankuna daban-daban na Najeriya, don haka ya ce kasar na bukace da zaman lafiya da kwanciyar hankali domin ci gaba.

Dangane da cece-kuce da fafutukar da wasu yankunan kasar suke yi na ganin tilas sai an ba su shugabancin kasar a shekara ta 2023, Janar Babangida ya ce ba ya goyon bayan tsarin na karba-karba, inda ya ce ko wane dan Najeriya na da damar tsayawa takara a kuma zabe shi daga ko wane yanki ya fito.

“A matsayi na na shugaba, ra’ayi na shi ne dan Najeriya kurum, ya zama shi ne shugaban Najeriya ko daga wane yanki ya fito.”

Babangida ya yi amfani da damar tattaunawar inda ya taya al’ummar musulmai murnar bikin karamar sallah ta bana.

Haka kuma ya jajantwa al’ummomi da dama da suka fuskanci kalubalen tsaro, musamman harin da ‘yan bindiga suka kai kan jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna.

Saurari tattaunawar Muryar Amurka da tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Babangida:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:39 0:00

XS
SM
MD
LG